U-21 Sai Ingila ta dage ta je gaba - Jordan Pickford

Jordan Pickford na kade fanaretin Linus Wahlqvis na Sweden Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Jordan Pickford ya kade fanaretin Linus Wahlqvist a wasan da suka yi canjaras da Sweden

Mai tsaron ragar tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Jordan Pickford ya ce dole ne sai sun yi nasara a ragowar wasansu biyu na gasar kofin kasashen Turai na rukuni, kafin su kai wasan kusa da karshe, wanda za su fara ranar Litinin da Slovakia.

Duk kasar da ta zama ta daya a kowane rukuni guda uku da ake da su, kai tsaye ta kai wasan na kusa da karshe, haka ita ma kasar da ta fi duk sauran da suka zo na biyu a rukunan, ta samu tikitin, inda za ta kasance cikammakin ta hudu.

Pickford wanda Everton ta saya fam miliyan 30 a kwanan nan ya kade bugun fanareti a wasan Ingilar na farko wanda ta yi canjaras da Sweden.

Slovakia ta doke mai masaukin baki Poland 2-1 a karawar da suka yi ranar Juma'a.

A ranar Alhamis ne Ingilar za ta fafata da mai masaukin bakin, Poland, wasan da golan ya ce, zai yi kyau, kuma daman abin da ya kai su kenan.

Pickford, mai shekara 23, ya ce ya yi farin ciki da aka kammala cinikinsa daga Sunderland zuwa Everton tun kafin gasar ta 'yan kasa da shekara 21 ta kasashen Turai, saboda hakan ya ba shi damar mayar da hankalinsa wuri daya kan wasan.