Zakarun nahiyoyi : Portugal ta yi 2-2 da Mexico

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo wanda ya bayar da kwallon farko aka ci, a ranar Juma'a wata majiya ta kusa da shi ta bayyana cewa yana son barin Real Madrid

Portugal ta tashi canjaras 2-2 da Mexico a gasar cin kofin kasashe na zakarun nahiyoyi a wasansu na farko da ake yi a Rasha.

Tun da farko an hana kwallon da Pepe ya ci saboda laifin satar-gida, bayan da alkalin wasa ya yi amfani da masu taimaka masa ta tsarin nan na amfani da hotun bidiyo domin tantance gaskiyar kwallo.

Bayan wannan ne kuma sai Ricardo Quaresma ya ci wa Portugal din a minti na 34, kafin kuma Javier Hernandez ya rama da ka a minti na 42.

Cedric Soares ne ya kara ci wa Portugal kwallo ta biyu a minti na 86, kwallon da minti biyar tsakani Hector Moreno ya farke bayan cikar minti 90 na wasan.

A ranar Asabar ne mai masaukin baki Rasha ta doke New Zealand 2-0 a daya wasan na rukuni na farko (Group A), bayan da shugaban Fifa Gianni Infantino ya bude gasar a filin wasa na St Petersburg.

Shugaban kasar Vladimir Putin da tsohon dan wasan Brazil Pele sun halarci bikin bude gasar.

Rukuni na daya (Group A) ya kunshi :

Rasha (saboda ita ce mai masaukin baki) da New Zealand da Portugal da Mexico.

Rukuni na biyu (Group B) ya kunshi :

Kamaru da Chile da Australia da Jamus (saboda ta dauki Kofin Duniya).