Kofin Zakarun Nahiyoyi : Chile ta casa Kamaru 2-0

Sanchez da Vidal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sanchez ( a hagu) ya dauko wa Vidal (a tsakiya) kwallon da Chile ta ci Kamaru ta farko

Chile ta doke Kamaru da ci 2-0 a wasan gasar cin kofin zakarun nahiyoyi da ake yi a Rasha, a rukuni na biyu (Group B) a ranar Lahadi.

Arturo Vidal ne ya ci Kamarun da ka bayan da Alexis Sanchez ya dauko masa wata kwallo da ka a minti na 81.

Ana dab da tashi ne kuma E. Vargas ya kara jefa kwallo ta biyu a ragar zakarun na Afirka, Kamaru.

Da wannan sakamakon Chilen ta zama ta daya a rukunin da maki uku yayin da Kamaru take ta karshe ba maki a wasa daya.

A ranar Litinin ne Australia za ta kara da Jamus a cigaba da wasan rukunin na biyu.

Kasashen da suka kasance zakaru a nahiyoyinsu su ne suke halartar gasar, amma kuma mai masaukin baki tana da tikiti kamar yadda kasar da ta dauki kofin duniya ita ma take da gurbi a gasar ta Confederation Cup.