Swansea City tana zawarcin Abraham na Chelsea

Tammy Abraham Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Abraham dan Ingila ne kuma yana cikin tagawar kasar 'yan kasa da shekara 21

Kulob din Swansea City yana son sayen dan wasan gaban kulob din Chelsea Tammy Abraham amma a matsayin aro.

Dan wasan mai shekara 19 wanda tsohon dan wasan kulob din Bristol City ne, ya buga wa kulob din wasa sau 26, inda ya zura kwallaye 26 a gasar kakar Championship ta bara.

Swansea City tana fatan cewa Abraham wanda ya taba yin aiki da koci Paul Clement yayin da yake kocin Chelsea, hakan zai iya sa dan wasan ya yi shawarar dawo wa Swansea.

Shugaban Swansea Huw Jenkins ya ce kulob din yana ci gaba da neman 'yan wasan tsakiya da kuma na gaba.

Sai dai ya ce suna duba yiwuwar karbo dan wasan Faransa, Bafetimbi Gomis, daga Marseille bayan ya tafi can a matsayin aro.

Labarai masu alaka