An yi jana'izar dan wasan Ivory Coast Cheick Tiote a Abidjan

Pallbearers at Cheick Tiote's funeral Hakkin mallakar hoto SIA KAMBOU/AFP/Getty Images
Image caption Tiote ya rasu yana da shekara 30

An yi jana'izar dan wasan Ivory Coast Cheick Tiote a Abidjan ranar Lahadi bayan ya rasu a China.

Tiote ya rasu ne yana da shekara 30 bayan fadi a lokacin atisaye a kulob dinsa na China Beijing Enterprises.

An karrama tsohon dan wasan tsakiyan Newcastle United da jana'izar soji, inda manyan mutane da 'yan wasa suka halarta.

An mayar da gawarsa gida Ivory Coast daga China a kwanakin baya.

Daruruwan mutane ne ciki har da tsohon kociyan tawagar Elephants, Herve Renard, suka je filin jiragin sama domin tarbar gawar Tiote a ranar Alhamis.

Cheick Tiote ya buga wa kasarsa fiye da wasanni 50. Kuma yana cikin tawagar Ivory Coast wadda ta lashe gasar kwallon kafa ta Afirka a shekarar 2015.

Wasu daga cikin tsoffin takwarorinsa 'yan wasa sun halarci jana'izar, ciki har da Salomon Kalou da ke wasa a Jamus.

Kalou ya ce labarin rasuwarsa ya tayar masa da hankali kaman sauran mutane.

Kalou ya shaida wa BBC cewar : "Wani ne wanda na girmama a matsayinsa na mutum da kuma dan wasan kwallon kafa."

"Na buga wasa da shi na shekara shida a tawagar kwallon kafa ta kasa kuma na hadu da shi a wasa a lokacin yana buga wa New Castle ni kuma ina buga wa Chelsea.

Saboda haka muna da mu'amala mai kyau da shi, kuma babu yadda zan kasa halartar jana'izarsa.

"Ba gaskiya ba ne. A yanzu haka ina ganin rasuwarsa kaman mafarki. Dukkanmu na nan ne domin mu nuna mishi kauna kuma mu nuna mishi cewar zai ci gaba da kasancewa zukatanmu," in ji Kalou.

Hakkin mallakar hoto SIA KAMBOU/AFP/Getty Images
Image caption Mutane sun nuna alhini kan mutuwar Cheick Tiote a wajen janai'zarsa a Abidjan ranar Lahadi

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba