Pep Guardiola na son sayo Dani Alves

Alves da Guardiola Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alves na daya daga cikin 'yan wasan da Guardiola ya fara saya da ya je Barcelona

Ga alama kociyan Manchester City Pep Guardiola zai nemi Juventus ta sayar wa kungiyarsa Dani Alves domin ya kara karfin bayansa.

A yanzu City ba ta da wani kwararren dan baya bayan da ta saki 'yan bayanta biyu Pablo Zabaleta da Bacary Sagna, wadanda kwantiraginsu da kungiyar ya kare.

A da dai ana rade-radin Guardiola zai dauko dan bayan Tottenham Kyle Walker ne amma kuma yanzu ana ganin yana duba yuwuwar sayo Alves, wanda ya yi wa Juventus wasa a lokacin rashin nasarar da ta yi da Real Madrid ta Kofin Zakarun Turai na bana a wasan karshe.

Ana tunanin Zakarun na Italiya na neman a ba su fan miliyan biyar kafin su rabu da Alves din dan Brazil mai shekara 34.

Guardiola ya san Alves sosai domin shi ya sayo dan wasan daga Sevilla a kan fan miliyan 23, ya kai shi Barcelona a shekarar 2008.

Tun daga lokacin tare suka dauki kofin La Liga uku da kofin kalubale na Spaniya biyu da na Zakarun Turai biyu, kafin Guardiola ya bar Nou Camp a 2012.