Sayen 'yan wasa: An tsuga wa Kungiyoyin China haraji

Diego Costa Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ba tabbas a zaman Costa a Chelsea bayan da ya ce kociyansu Antonio Conte ya gaya masa cewa ba ya cikin tsarin kungiyar

Kungiyoyin kwallon kafa na China na fuskantar biyan harajin kashi dari bisa dari na kudin sayen 'yan wasa yayin da aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta tsakiyar kaka a ranar Litinin.

Hukumar kwallon kafa ta kasar ta Sin ta dauki matakin ne a kan kungiyoyin da suke faduwa maimakon samun riba, domin ta yi maganin yadda kungiyoyi ke kashe makudan kudade wurin sayen 'yan wasan waje.

Kungiyoyin wasan kasar sun kashe fan miliyan 331 a lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta kasar ta lokacin huturu, wanda kudin ya zarta wanda kungiyoyin Premier suka kashe a watan Janairu.

Idan har matakin biyan harajin ya tabbata, to hakan na nufin duk dan wasan da kungiyar kasar za ta saya sai ta linka kudin cinikin nasa biyu kenan, inda harajin zai tafi wani asusun gwamnati.

Dan wasan gaba na Manchester United Wayne Rooney da na Chelsea Diego Costa na daga fitattun 'yan wasan da ake rade-radin za su tafi China, yayin da kasuwar ta bude har zuwa ranar 14 ga watan Yuli.