Kofin Zakarun Nahiyoyi: Jamus ta doke Australia 3-2

'Yan wasan Jamus na murnar cin kwallo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Har yanzu Jamus ba ta taba cin Kofin Zakarun Nahiyoyi ba

Masu rike da kofin duniya Jamus sun doke Australia a birnin Sochi na Rasha, nasarar da ta kasance ta farko da suka yi a gasar kofin Zakarun Nahiyoyi a cikin shekara 12.

Lars Stindl ne ya fara ci wa Jamus kwallo a minti biyar da shiga fili kafin dan wasan Celtic Tom Rogic ya farke wa Australia a minti na 41.

Wasa bai yi nisa ba daga nan, a minti na 44 Julian Draxler ya ci wa Jamus ta biyu da bugun fanareti bayan da dan wasan QPR Massimo Luongo ya doke Leon Goretzka kafin kuma Goretzka ya sake ci wa Jamus ta uku a minti na 48.

Kociyan Jamus Joachim Low ya sanya sabbin 'yan wasan da ba su taba taka wa kasar leda ba a cikin tawagar da ya je da ita gasar a Rasha, bayan da ajiye gwanin mai tsaron raga Manuel Neuer da dan wasan tsakiya na Arsenal Mesut Ozil da dan baya Mats Hummels da dan gaba Thomas Muller.

Jamus za ta yi wasanta na gaba ne na rukunin na biyu (Group B) da Chile, wadda ta doke Kamaru 2-0 ranar Lahadi, ranar Alhamis a birnin Kazan.

Ita kuwa Australia za ta kara da Kamaru ne ranar Alhamis din a birnin St Petersburg.

Yanzu Chile ce ta daya a rukunin nasu bayan wasa dai-dai, da maki uku da kuma kwallo biyu.

Jamus tana matsayi na biyu ita ma da maki uku amma da kwallo daya.

Sai Australia ta uku ba maki, da bashin kwallo daya a ragarta, yayin da Kamaru take ta hudu ita ma ba maki, kuma da bashin kwallo biyu.