Tennis: Shekaru sun sa Andy Murray ya karaya

Andy Murray Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Murray na fatan cin gasar Aegon a karo na shida zai karfafa masa guiwar kare kofin Wimbledon

Gwanin tennis na daya a duniya dan Birtaniya Andy Murray ya ce kila dai 'yan shekaru kadan ne suka rage masa na kasancewa gwani a fagen wasan, amma ya ce zai yi kokarin galaba a duk gasar da ya shiga.

Murray wanda ya kai shekara 30 a yanzu yana fatan cin gasar tennis ta Wimbledon ne a karo na uku, inda yake son zama daidai da Fred Perry, wanda ya kafa wannan tarihi, idan an fara gasar a wata mai zuwa.

Andy Murray ya yi furucin ne a wata hira da BBC inda yake nuna cewa duk da yadda 'yan wasa ke ci gaba da shiga gasa bayan sun kai shekara 30, shi kam yana ganin da wuya ya dade yana cigaba da wasan a wadannan shekaru da tagomashin da aka san shi da shi.

Dan wasan ya ce idan ya yi nasara a karo na shida a gasar Aegon Championship a Landan, yana fatan hakan zai zama matakin kare kofinsa na Wimbledon, wanda zai zama na uku.

A ranar Talata ne mai rike da kofin gasar ta Landan wadda aka fara ranar Litinin, zai kara da dan uwansa dan Birtaniya Aljaz Bedene a zagayen farko na gasar a filin wasa na Queen's Club.

Murray dan yankin Scotland wanda ya samu lambar girmamawa ta Sarauniya a lokacin bikin bayar da lambobin na sabuwar shekara, a watan Mayu ne ya cika shekara 30, kuma dukkanin manyan gwanayen tennis din na duniya maza su biyar sun dara shekara 30.

Rafael Nadal na Spaniya yana da 31 da Stan Wawrinka na Switzerland mai 32, Novak Djokavic na Serbia yana 30 yayin da Roger Federer shi ma dan Switzerland yake da shekara 35.