Damben Boksin: Tim Hague ya mutu bayan dukan kawo-wuka

Tim Hague Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Dambe hudu kawai Tim Hague ya yi tun lokacin da ya sauya sheka zuwa wasan, kuma an doke shi a uku bayan nasara a na farko

Tsohon dam damben hannu da kafa Tim Hague ya mutu yana da shekara 34 bayan da aka yi masa dukan kawo-wuka a wani damben boksin a Canada ranar Juma'a.

Dan Canadan, wanda ya fafata a gasar damben hannu da kafa na UFC daga 2009 zuwa 2011, sau biyar ana kai shi kasa a turmi biyu na farkon dambensa da Adam Braidwood kafin a tsayar da damben.

Da kafarsa ya fita daga fagen damben amma kuma aka kai shi asibiti daga bisani, inda kuma a can ne ya shiga halin rai kwakwai-mutu-kwakwai.

A ranar Lahadi ne iyalansa suka fitar da sanarwar mutuwar ta Tim.

A karawarsa ta farko a damben hannu da kafa Hague ya doke Pat Barry, amma kuma tun daga nan bai sake yin nasara ba a dukkanin irin wannan damben da ya yi guda hudu a gaba.

Bayan da ya koma damben boksin ma kuma hakan ya yi, inda ya doke Patrick Graham a wasansa na farko amma kuma aka doke shi a sauran dambe uku da ya yi, wadanda suka hada da dukan kawo-wuka biyu da 'yan uwansa 'yan Canada Mladen Miljas da Braidwood.