Ana tuhumar Luka Modric da shedar zur

Luka Modric a kotu Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Idan an same Modric da laifi zai iya zaman gidan kaso na wata shida zuwa shekara biyar

Hukumomin kasar Crotia suna binciken kyaftin din kasar kuma dan wasan Real Madrid Luka Modric kan zargin yin shedar zur.

Ana zargin dan wasan na tsakiya ne da bayar da bayanan karya a shari'ar zambar kudin haraji da ake yi wa tsohon kociyansa a kungiyar Dinamo Zagreb, Zdravko Mamic.

Ana zargin Mista Mamic da dan uwansa Zoran Mamic da kuma wasu mutanen biyu da almundahanar da ta jawo wa kungiyar ta Dinamo Zagreb asarar kusan euro mliyan 17.

Yayin da ita ma gwamnatin kasar ta rasa euro miliyan 1.5 a sanadin zambar, daga harkar sayar da 'yan wasa.

Idan har an samu dan wasan da laifi zai iya zaman gida yari na tsakanin wata shida da shekara biyar.