An sake zabar Florentino Perez shugabancin Real Madrid

Florentino Perez and Cristiano Ronaldo at Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Florentino Perez ya fara wa'adinsa na biyu a matsayin shugaban kungiyar a shekarar 2009 lokacin Madrid na gaf da sayan Cristiano Ronaldo

Florentino Perez zai ci gaba da jan ragamar kulob din Real Madrid bayan an sake zabensa a matsayin shugaban kungiyar.

Perez mai shekara 70, wanda ya ke wa'adinsa na biyu a matsayin shugaba, ya tsaya takara ba tare da hamayya ba.

Perez ya fara rike mukamin ne tsakanin shekarar 2000 zuwa 2006, a lokacin da Real Madrid ta sayi Luis Figo da David Beckham da kuma Ronaldo.

Ya koma mukamin a shekarar 2009, a lokacin da kungiyar ta sayi Cristiano Ronaldo da Kaka da Karim Benzema da kuma Xabi Alonso.

A halin yanzu dai makomar Cristiano Ronaldo a Bernabeu na cike da rashin tabbas bayan ya sanar da cewa yana son barin kungiyar.

Perez ya dauki kociya shida aiki a lokacin wa'adinsa na farko yayin da Madrid ta lashe gasar La Liga biyu da kuma Gasar Zakarun Turai.

Ya yi murabus a watan Fabrairun shekarar 2006 bayan kungiyar ta shafe shekara uku ba tare da lashe wani muhimmin kofi ba.

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba