Nigeria: Osinbajo zai gana da shugabanni daga Arewa

Osinbajo da shugabannin gargajiya Hakkin mallakar hoto Gwamnatin Najeriya
Image caption Farfesa Osinbajo dai ya yi gargadin cewar gwamnati za ta kama masu kalaman kiyayya

Ana sa ran mukaddashin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo zai yi wata ganawa da shugabanni daga arewacin kasar a fadar gwamnati da ke birin Abuja a ranar Talata.

Babban mai taimakawa mukaddashin kan harkar yada labarai, Laolu Akande ne ya bayyana hakan a shafinsa na tweeter, inda ya ce ganwar za ta hada da shugabannin al'ummar Musulmai da kuma na Kiristoci.

Ganawar ba ta rasa nasaba da ci gaba da tuntubar juna da Farfesa Osinbajo ke yi domin a kawo karshen kalaman kiyayya da wasu ke yadawa a kasar.

A ranar Litinin da maraice ne dai mukaddashin shugabana kasar ya yi wani taron buda baki da shugabannin a Abuja.

Haka zalika, taron na zuwa ne a lokacin da batun fafutukar kafa kasar Biafra da kuma wa'adin da wata kungiyar matasa ta arewacin Najeriya ta bai wa 'yan kabilar Igbo na ficewa daga yankin ke ci gaba da janyo cece-kuce a kasar.

Bayan wannan ne shugaban ya gana shugabannin al'umma daga yankin kudu masi gabashin kasar.

Daman ya gana da shugabannin al-umma daga yankin kudu maso kudancin kasar domin tabbara da dorewar zaman lafiya.

Batun masu fafatukar kafa kasar Biafra dai ya rarraba kawunan jama'a inda wasu ke goyon bayan kuma wasu ba sa goyon baya.

Babu tabbacin cewar ganawar da mukaddashin shugaban kasar ke yi yanzu da shugabannin al-umma zai rage zaman dar-dar din ake yi wasu sassan kasar.

Labarai masu alaka