Salah ya kusa zama dan wasan Afirka mafi tsada a tarihi

Mohamed Salah Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Mohamed Salah na dab da zama dan wasan Afirka mafi tsada a tarihi

Liverpool ta kusa kammala yarjejeniyar sayen dan wasan gefe na kungiyar Roma da Masar Mohamed Salah kan kudin da ba ta taba sayen wani dan wasa ba, fan miliyan 40.

Dan wasan mai shekara 25 ya kasance na gaba-gaba da kociyan kungiyar Jurgen Klopp yake son sayowa, kuma zai iya zarta kudin da Liverpool ta sayo Andy Carroll fan 35 a shekarar 2011.

Yanzu dai ana ci gaba da tattaunawa kan cinikin, kuma dan wasan yana cike da farin cikin sake dawowa gasar Premier bayan zaman da ya yi a Chelsea wanda bai yi masa armashi ba.

Idan cinikin ya zarta fan miliyan 34 da Liverpool ta sayo Sadio Mane, Salah zai kasance dan wasan Afirka mafi tsada.

A shekara ta 2014 dan was an na Masar ya kusa zama na Liverpool, amma Chelsea ta saye shi daga Basle a kan fan miliyan 11.

Chelsea ta bayar da aronsa ga Fiorentina daga baya kuma ta mika shi ga Roma,kafin kuma Roman ta saye shi gaba daya a kan kusan fan miliyan 15 a bazarar da ta wuce.

Salah na daga cikin 'yan wasan da suka taka wa Roma rawa sosai ta gama gasar Serie A a matsayin ta biyu a kakar da ta kare, inda ya ci kwallo 15 a wasa 31 da ya yi mata.

Tuni daman Liverpool ta dauki dan wasan gaba na Chelsea Dominic Solanke, mai shekara 19, wanda ya zama dan kwallon da ya fi cin kwallo a gasar da Ingila ta ci kofin duniya na 'yan kasa da shekara 20, kuma a ranar 1 ga watan Yuli zai je kungiyar.