Perez zai tattauna da Cristiano Ronaldo

Florentino Perez da Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Perez ya ce ba za su bari maganar kudi ta sa Cristiano ya bar Madrid ba

Shugaban Real Madridino Florentino Perez ya ce zuwa yanzu bai yi magana da Cristiano Ronaldo kan zamansa a kungiyar ba amma zai tattauna da shi bayan gasar cin Kofin Zakarun Nahiyoyi.

Shi dai Ronaldo, mai shekara 32, an bayar da rahotannin cewa yana son barin Spaniya ne bayan hukumomi sun zarge shi da yin zambar kudin haraji.

Dan wasan wanda yake tare da tawagar Portugal a gasar da ake yi yanzu a Rasha, ya kulla sabuwar yarjejeniyar zama a Madrid ta shekara biyar a watan Nuwamba na 2016, amma kuma ana maganar cewa zai koma Manchester United.

Da aka tambayi Perez, wanda a ranar Litinin aka sake zabarsa, sai ya ce shi dai abin da zai iya cewa yanzu kawai shi ne Cristiano Ronaldo dan wasan Real Madrid ne.

Shugaban ya ce ba ya son ya yi wani abu a yanzu da zai shafi tawagar ta Portugal a gasar da take yi a Rasha.

Amma ya ce lalle kam wani abu ya faru, kuma wannan abin ya shafi dan wasan, kimarsa.

Perez ya ce dan wasan yana son kawai ya zama mai taka ledar da ya fi kowa a duniya.

Kuma idan har Cristiano zai bar Madrid to ba zai zama saboda kudi ba in ji Perez.

Masu gabatar ta kara na Spaniya sun zargi Ronaldo da zambatar hukumomin kasar miliyoyin euro na haraji, zargin da ya musanta.