An sa Sunderland a kasuwa bayan ta fadi daga Premier

Filin wasan kungiyar Sunderland Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Faduwar Sunderland daga Premier ta kawo karshen zamanta na shekara 10 a gasar

Mutumin da ya mallaki Sunderland, Ba'amurke Ellis Short na dab da sayar da kungiyar inda yake duba tayin da ya samu daga bangarori biyu.

Wani kamfanin Jamus da kuma Ben Turner and Leo Pearlman daga kamfanin harkar hada fina-finan talabijin Fulwell 73 ne suka taya kungiyar.

A ranar Juma'a ne Sunderlanda ta tabbatar cewa tana ci gaba da tattaunawa da wadanda suka bayyana aniyarsu ta sayen kungiyar.

Mista Short wanda ya mallaki kungiyar tun 2009 yana son sayar da ita ne bayan da ta fadi daga gasar Premier.

Sunderland na son ganin an kammala tattaunawar a kan lokaci, domin har ta sanya wa'adin gama cinikin, tare da bayar da muhimmanci kan neman wanda zai maye gurbin David Moyes kociyan da ya bar kungiyar a watan Mayu.