Fifa ta yaba da amfani da bidiyo don taimaka wa lafiri

Alkalin wasa Mark Geiger ya nemi da a yi amfani da fasahar bidiyo a wasan Australiya da Jamus Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Alkalin wasa Mark Geiger ya bukaci da a duba bidiyo domin tantance kwallo ta biyu ta Australia da Tomi Juric, ya ci Jamus

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta yaba da tsarin amfani da hotunan bidiyo domin taimaka wa alkalin wasa a gasar cin kofin Zakarun Nahiyoyi, da cewa fasaha ce da za ta zama bangaren wasan nan gaba.

Ya zuwa yanzu dai an yi amfani da fasahar sau biyar a gasar cin Kofin Zakarun Nahiyoyi a Rasha, inda a wani lokacin tsarin ke haifar da rudani ga 'yan kallo.

Shugaban Fifa Gianni Infantino ya ce, sun ga yadda tsarin ke taimaka wa alkalan wasa su yanke hukuncin da ya dace.

Ya kara da cewa yana matukar farin ciki da hakan ya zuwa yanzu.

A watan Disamba da ya wuce ne aka fara amfani da fasahar a wata gasar Fifa lokacin wasa cin Kofin Duniya na kungiyoyi a Japan, kuma tun daga nan ake amfani da ita a wasu wasannin da aka zaba a gwada.

A makon da ya gabata ne Ingila ta fara cin moriyar fasahar lokacin da aka yi amfani da ita aka kori dan wasan baya na Faransa Raphael Varane, a lokacin wasansu na sada zumunta a Paris.

Haka kuma an hana kwallon da dan wasan baya na Portugal Pepe ya ci, da wadda Eduardo Vargas na Chile ya ci Kamaru, saboda an gano cewa an yi satar gida bayan da aka yi amfani da fasahar, a gasar kofin Zakarun Nahiyoyin a Rasha.