Tennis: An yi waje da Andy Murray a gasar London

Na daya a duniya a tennis Andy Murray Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun watan Nuwamba Andy Murray yake rike da matsayin na daya a tennis a duniya

An yi waje da gwanin tennis na daya a duniya, kuma mai rike da kofin gasar Aegon Championship a zagayen farko na gasar a London.

Jordan Thompson na Australia, na 90 a duniya wanda ya maye gurbin Aljaz Bedene da ya ji rauni, shi ne ya fitar da zakaran na duniya Andy Murray da ci 7-6 (7-4) 6-2.

Nasarar ita ce mafi girma da Jordan mai shekara 23 ya yi a rayuwarsa ta wasan tennis, kuma ya yi ta ne bayan sa'a daya da minti 43.

Kuma da farko tun a lokacin fitar da wadanda za su wakilci Australia a gasar aka yi waje da shi, amma yanzu aka kawo shi domin ya maye gurbin Bedene wanda ya ji rauni a wuyan hannunsa.

Wannan shi ne karon farko tun 2012 da Murray mai shekara 31, dan Birtaniya ya yi rashin nasara a wasansa na farko na gasar.

Murray dan yankin Scotland yana daukar kofinsa na Wimbledon ne a 2013 da 2016 bayan ya zama zakara a gasar da ake yi a Queen's Club.

Haka shi ma gwani na biyu a gasar Stan Wawrinka da na uku Milos Raonic duk sun yi rashin nasara a zagayen farko na gasar ta London.