Kofin Zakarun Turai: Uefa ta ba RB Leipzig dama

Magoya bayan RB Leipzig Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sau hudu Leipzig ta samu zuwa gasa ta gaba da kuma gurbin zuwa gasar Zakarun Turai a shekara takwas

Hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa ta tabbatar cewa kungiyar RB Leipzig da Red Bull Salzburg dukkaninsu za su yi wasa a gasar Zakarun Turai.

Dukkanin kungiyoyin biyu suna da kwakkwarar alaka ne da kamfanin lemon nan mai kara kuzari ne Red Bull, kuma bisa doka Uefa ta hana kungiyoyin da ke da alaka sosai da juna su yi wasa a wata gasarta a kaka daya.

Hukumar ta Uefa ba ta son wani kamfani ko hukuma ta mallaki kungiyoyi biyu da ke cikin gasa daya.

Idan haka ta kasance ana bayar da fifiko ne ga kungiyar da ta kasance zakara a gasar kasarta, wanda da an bi hakan Leipzig ba za ta samu shiga gasar Zakarun Turan ba.

To amma yanzu hukumar ta kwallon kafar ta Turai ta warware wannan matsala da ake ganin za ta shafi kungiyoyin biyu.

Kungiyar RB Leipzig wadda ta zo ta biyu a gasar Bundesliga ta Jamus a kakar da ta kare da kuma zakarun gasar Austria Salzburg, dukkanninsu sun samu damar zuwa gasar ta Zakarun Turai mai zuwa ta kakar 2017-18.

A shekara ta 2009 aka kafa kungiyar Leipzig tare da goyon bayan kamfanin lemon na Red Bull, kuma ta yi nasarar hauro matakin gasa hudu a cikin shekara bakwai, kafin ta zama ta biyu a babbar gasar kasar ta Bundesliga.

Za a iya daukaka kara a kan hukuncin na Uefa a kotun kararrakin harkokin wasanni ta duniya nan da kwana goma.