Mexico ta roki magoya bayanta kan wakokin kyamar 'yan luwadi

'Yan wasan Mexico na murnar cin kwallo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mexico ta yi canjaras 2-2 da Portugal a wasansu na farko na gasar zakarun nahiyoyin

Hukumar kwallon kafa ta Mexico ta roki wasu magoya bayan tawagar kasar da su daina wata waka da suke yi wadda hukumar kwallon kafa ta duniya ta ce ta kyamar 'yan luwadi ce.

Hukumar ta yi kiran ne bayan da Mexico ta yi canjaras da Portugal a wasan cin kofin zakarun nahiyoyi da ake yi a Rasha.

Fifa ta gargadi hukumar kwallon kafa ta Mexico a kan wakokin da cewa za ta dauki mataki a kai idan magoya bayan suka kara aikata laifin.

Daman tuni Fifa ta ci tarar Mexico sau takwas a lokacin wasannin neman zuwa gasar kofin duniya, saboda yin wakokin kyamar masu neman jinsi daya.

Wasu magoya bayan tawagar Mexico sukan yi wa masu tsaron raga wadannan wakoki da ake cewa na kyamar masu neman jinsi daya, idan za su buga kwallo.

A yau ne Mexico za ta fafata da New Zealand yayin da Rasha mai masauki baki za ta kara da Portugal a gasar cin kofin zakarun nahiyoyi.