'Abin takaici ne Manchester United ba ta da kungiyar mata'

Rachel Brown-Finnis, mai yi wa BBC sharhin wasanni
Image caption Abin takaicin duk lokacin da ka tambayi dali Man United ba ta da wani dalili mai gamsarwa na rashin kungiyar wasan mata

Abin mamaki ne a ce a 2017 babbar kungiya kamar Man United ba ta da tawagar mata masu kwallo kuma babban abin takaicin ma ba za su iya bayar da wani dalili mai gamsarwa ba kan hakan.

Rachel Brown-Finnis mai yi wa BBC sharhin wasanni kenan ta yi wannan furuci kan rashin wata kungiyar kwallon kafa ta mata ta Manchester United kamar yadda sauran kungiyoyi suke da.

Mai sharhin ta ce ka duba kasashen duniya, za ka ga duk wata babbar kungiyar kwallon kafa tana da kungiyar 'yan wasa mata, ko kuma tana shirin kafawa.

Manyan kungiyoyi biyu, wadanda suka yi wasan karshe na cin kofin Zakarun Turai Real Madrid da Juventus, suna dab da kafa nasu kungiyoyin na mata. In ji ta.

Brown-Finnis ta ce yawancin wadannan kungiyoyin mata an shigar da su cikin takwarorinsu maza kuma su ma ana ba su kudade yadda ya kamata.

Ta kara da cewa misali, a nan kusa ba nesa ba daga OldTrafford, yadda Manchester City take karfafa kungiyarta ta mata abu ne da yake na karfafa guiwa da misali.

Southampton ce kadai a gasar Premier da ba ta da kungiyar 'yan wasa mata, ko da yake ba dadewa ta sanar da kafa sabuwar kungiyar mata 'yan kasa da shekara 21 domin wasannin kaka mai zuwa, wanda hakan wata dama ce ga matasan 'yan wasan kungiyar mata, abin da matan Manchester United ba su da shi.

Mai sharhin wasannin ta BBC ta ce duk a matakin da Manchester United ta kwatanta kanta da wasu kungiyoyi a Ingila ko Birtaniya ko ma duniya, tana mayar da kanta baya a dangi ne, a wannan fanni na wasan mata.

Ta ce duk wanda ya tambayi hukumomin kungiyar ta Manchester United kan dalilin da ya sa ba su da kungiyar wasa ta mata, wanda kuma shekara da sheakaru ana tambayarsu, sai ka ji sun ce maka suna duba lamarin.

A da akwai kungiyar mata ta Manchester United kafin wadanda suka mallaki kungiyar (TheGlazers) ya rushe ta a shekarar 2005, inda mai magan da yawun kungiyar ya ce ba ta cikin tsarin harkarsu.