Tennis: An fitar da Jo-Wilfried Tsonga a London

Jo-Wilfried Tsonga Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Bafaranshe Jo-Wilfried Tsonga, shi ne ya zo na biyu a gasar a shekara ta 2011

Jo-Wilfried Tsonga ya zama gwanin dan wasan tennis na gaba da aka yi waje da shi a gasar Aegon Championships da ake yi a Landan, inda Gilles Muller na Luxembourg ya fitar da shi.

An fitar da Tsonga dan Faransa wanda shi ne gwani na biyar a gasar a zagaye na biyu na da ci 6-4 6-4 a jere.

Ficewar Tsongan ta biyo bayan ta gwani na daya a duniya, kuma mai rike da kofin gasar Andy Murray na Birtaniya da Stan Wawrinka da kuma Milos Raonic, manyan gwanaye uku a gasar, ranar Talata.

Tsonga wanda shi ne ya zama na biyu a gasar ta 2011, ya karbi sakamakon a matsayin kaddara da cewa, haka wasan ya gada, ''wani lokaci ka yi iya kokarinka, amma ba yadda za ka yi saboda wanda kake fafatawa da shi yana wasa da kyau.''

Muller mai shekara 34 wanda ya dauki kofin gasar s-Hertogenbosch ta Netherlands a makon da ya wuce, yanzu zai hadu da wanda ya fitar da Murray Jordan Thompson ko kuma Sam Querrey.

Dan tennis din wanda shi ne gwani na 26 a duniya, ya kai wasan dab da na kusa da karshe a shekara uku a jere.

Dimitrov takes on France's Julien Benneteau later on Wednesday, before Czech seventh seed Tomas Berdych plays Canadian teenager Denis Shapovalov.