Tennis: Victoria Azarenka ta yi nasara a wasan farko bayan haihuwa

Victoria Azarenka Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Victoria Azarenka ta dauki kofi 20 a rayuwarta

Tsohuwar gwana ta daya a duniya a wasan tennis Victoria Azarenka ta yi nasara a wasanta na farko da ta dawo bayan shekara daya da ta yi hutu domin haihuwar danta.

Azarenka wadda sau biyu ta dauki kofin Australian Open wadda kuma ta haifi danta Leo a watan Disamba ta doke Risa Ozaki ta Japan a gasar ta Mallorca Open da ci 6-3 4-6 7-6 (9-7).

Wasan shi ne na farko tun lokacin da Azarenka mai shekara 27 'yar kasar Belarus ta yi tun bayan da aka doke ta a gasar Faransa a watan Yuni na 2016.

Azarenka ita ce gwana ta shida a duniya a tennis lokacin da ta bayyana cewa tana da juna biyu a watan Yuli na bara.

Saura kiris ya rage a fitar da ita daga gasar a ranar Talata saboda matsalar fitulu da aka samu a filin wasan, abin da ya sa aka dage wasan, amma da aka dawo ranar Laraba ta farfado ta doke Ozakin gwana ta 74.