Zakarun Nahiyoyi : Portugal ta ci Rasha 1-0, Mexico ta doke New Zealand 2-1

Lokacin da Ronaldo ya ci Portugal Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kwallo ta 74 da Ronaldo ya ci wa Portugal, kuma ta 603 da ya ci gaba daya a wasanninsa

Portugal ta doke Rasha da ke karbar bakuncin gasar kofin zakarun nahiyoyi 1-0, a wasa na biyu na rukuni na daya (Group A) ranar Laraba.

Cristiano Ronaldo ne ya ci kwallon da ka a minti na takwas da shiga fili.

Kwallon da ya ci ita ce ta 74 da ya ci wa kasarsa, kuma ta 603 da ya ci gaba daya a wasanninsa.

Sannan kuma yanzu ya kasance ya zura kwallo a raga a manyan gasa daban-daban har takwas.

Sakamakn Wasan Mexico da New Zealand:

A daya wasan na rukunin na daya Mexico ta doke New Zealand da ci 2-1, wanda sakamakon ya sa Mexicon ta zama a saman teburinsu.

Mexico tana ta daya yanzu da maki hudu, yayin da Portugal ta dawo ta biyu ita ma da maki hudu, kowacce da bambancin kwallo dai-dai.

Rasha mai masaukin baki ita ce ta uku da maki uku, yayin da New Zealanda ta kasance ta hudu (karshe) ba maki a wasa biyu da kowace kasa ta yi a rukunin.

A wasansu na farko Portugal ta tashi 2-2 da Mexico, yayin da Rasha ta ci New Zealand 2-0.

Wannan ya sa Rasha ta dawo matsayi na uku da maki, yayin da New Zealand take ta hudu (karshe) ba maki ko daya.