Yadda 'yan kwallo Musulmai ke jure taka leda a lokacin azumi

Palestine football fans Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasan neman shiga gasar Asiya tsakanin Falasdinu da Oman tsakanin kasashen musulmi biyu wasa mai kalubale

An buga wasannin kasa da kasa na wannan makon jiya ne cikin watan Ramadan, lokacin da Musulmai a fadin duniya ke azumin wata daya.

Dole kociyoyin kasasen da mafi yawansu Musulmai ne su nemi dabarun taimaka wa tawagar 'yan wasansu, wadanda yawancinsu ke azumi daga sanyin safiya zuwa maraice.

Watan Ramadan ya zo daidai da gasar Olympics da aka gudanar a birnin Landan a shekarar 2012, da gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014, da kuma gasar cin kofin Turai ta bara wadda aka yi a Faransa. Saboda ranukun lokacin zafi masu tsawo a Turai, yanayin iya taka ledan dan wasa ka iya zama wani abun dubawa.

A lokacin gasar Olmpics da aka yi a birnin Landan a shekarar 2012, tawagar kwallon kafa ta Haddadiyar Daular Larabawa ta samu fatawa daga hukumar koli ta addini a kasar cewar kar 'yan wasan su yi azumi a ranakun wasa. Dan wasan Jamus, Mesut, shi ma ya zabi shan azumi lokacin da yake taka wa kasarsa leda a gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil.

Amma wasu sun hakikance kan yin azumi. Da yawa daga cikin 'yan tawagar kasar Aljeriya sun yi azumi yayin wasansu na zagaye na biyu da Jamus a gasar, duk da cewar hukumomin addini sun ba su fatawa ta musamman cewar su sha azumin. Amma mai tsaron gida, Rais M'bolhi ya karya azuminsa da dabino da ruwa bayan hutun rabin lokaci.

Me nene Ramadan?
Shi ne wata na tara a Musulunci, lokacin da ake azumi daga sanyin safiya zauwa maraice.
Musulmai sun yi imanin cewar duk wani aikin alkhairi a watan yana samar da karin lada a domin Allah Ya albarkaci watan.
Wasu za su kara kaimi wajen sallah, a lokacin da wasu za su lazimci karanta al-qur'ani.
Kwanan watan na sauyawa tare da rage kwana 11 a ko wace shekara.
Ana gudanar da sallar Idi a karshen watan na Ramadan.

Bana Ramadan ya kama ne daga 26 ga watan Mayu zuwa 24 ga watan Yuni, kuma tawagogin kwallon kafa na kasase da dama a Asiya da Afirka sun jinkirta fara wasanninsu zuwa cikin dare. Wasan neman shiga gasar cin kofin Asiya tsakanin Falasdinu da Oman da aka buga a makon jiya daya ne daga cikin wasannin da suka ba da kalubale matuka.

A da dai hukumar kwallon kafa ta Falasdinu ta ce za a buga wasan ne da karfe 9.45 na yammacin Talata, amma an daga wasan zuwa karfe 10.45 na dare, inda daga baya ta daga wasan zuwa karfe 11.00 na dare.

An dau matakin daga lokacin wasan ne domin bai wa tawagar da magoya bayanta damar bude baki kafin zuwa filin wasa, amma kuma sai matakin ya bai wa magoya bayan tawagar daga birnin Kudus da Ramalla ciwon kai.

Hukumar kwallon kafa ta Falasdinun ta nemi jan hankalin magoya baya kungiyar da su halarci wasan ta hanyar dauke kudin shiga filin wasa, amma domin mutane daga arewaci da kuma yammacin gabar yamma ta kogin Jodan da kuma manyan biranen Falasdinawa suna bukatar sa'o'i biyu na hawa mota zuwa filin wasa, akwai fargabar cewar ba za a samu isassun mutane a filin wasan ba.

Daga mahangar shirya wa wasan kasasen Oman ad Falasdinu sun daga atisayensu zuwa dare kuma suka sauya irin abincin da suke ci.

Bader Aqel, daya daga cikin likitocin Falasdinu, ya ayyana sauye-sauyen da aka yi wa harkar atisayen tawagar kwallon kafa ta kasar a lokacin Ramadan.

"Mun tabbatar wa 'yan wasan cewar su sha akalla lita uku na ruwa bayan buda baki domin su samu isasshen ruwa a jiki."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ramadan ya kama ne daga 26 ga watan Mayu zuwa 24 ga watan Yuni a bana, kuma lokaci ne ibada da azumi

Bayan Ramadan za a ba wa 'yan wasan abinci iri-iri yadda za su debi abin da ya gamshe su - amma a makon jiya Aqel da sauran jami'an kiwon lafiya na tawagar sun lura da abin da 'yan wasan ke ci, suna ba su abinci a kwano domin hana su ci da yawa.

An bai wa 'yan wasan abinci mai kara kuzari kamar shinkafa iri daya da abinci mai gina jiki kadan da kuma ganye. An tsara abincin ne domin samar wa 'yan wasan abincin da zai yi saurin narkewa kuma mai kuzari.

A mafi yawan lokuta, jam'ian horar da 'yan wasan sukan tafi dakin motsa jiki sa'a daya kafin bude baki domin tayar da aikin narkar da abincin bayan shafe wuni ba tare da irin wannan aikin ba.

Aqel ya ce: "Abu mafi muhimmanci shi ne kar 'yan wasan su tsaya a wuri daya da rana. Muna son mu kauce wa yawaita barci ga 'yan wasan [lamarin da ke yawan faruwa cikin azumi]."

'Yan wasan Falasdinu na fara atisayensu ne da karfe 11 na dare, bayan wannan 'yan wasan su kan koma dakunansu na otel domin wanka da kankara da kuma motsa jiki kafin su yi sahur da misalin karfe 2:45 na safe.

Pim Verbeek - dan kasar Neatherlands da ke jagorantar Oman - yayi ta fuskantar kalubale da tawagar 'yan kasa da shekara 23 na kasar Moroko kuma ya sauya yanayin atisayinsa ta yadda zai fi dacewa da 'yan wasan.

Ya shaida wa BBC cewar: "Da gaske ya bambanta. za ka yi atisayi ne sau daya a yini daya. Za ka fi so ka yi sau biyu inda dama. Atisayenmu na yamma ya yi kyau, kuma muna adana kuzarinmu ne kafin wasan."

Mai tsaron gidan Reading, Ali Al Habsi, shi ne keftin din Oman. Yana ganin cewar jinkirta wasa ya fi wa 'yan wasan - yana basu lokacin mayar da abin da jikinsu ya rasa, da kuma hutu bayan azumin sa'o'i 17 wanda ake fara wa daga karfe 3:50 na safe zuwa 7:45 na yamma.

Ya ce :"Mako biyun da muka yi a sansanin shirya wa wasan sun taimaka mana domin mu saba da wasa cikin azumi. Mu yi atisaye a dai-dai lokacin da za a buga wasan domin wannan ya sa mu ci karfin duki wani kalubalen da Ramdana zai iya kawo mana."

Hakkin mallakar hoto Empics
Image caption Kungiyar Al Habsi ta sha kaye a wasan karshe, kuma dan wasan bai yi azumi ba domin wasan

Al Habsi shi kadai ne dan wasan da ya zame wa dole ya yanke shawara kan ko zai sha azumi ko ba zai sha ba, a lokacin da ya ke buga wa kungiyar kwallon kafarsa tamola. A shekaru 14 da ya yi a Turai da kungiyar Lyn Oslo da Bolton Wanderers da Wigan Athletic da kuma Reading sau daya ne kawai batun ya tashi, a yayin da Reading ta kara da Huddersfield Town a wasan karshe na gasar Championship da aka buga a watan jiya. Al Habsi, wanda tsohon dan kwana-kwana ne, ya zabi shan azumi.

Yadda Falasdinu take gudanar da atisayenta - wanda ya yi hannun riga da na Oman, ba a bai daya yake ga dukkan 'yan wasa ba.

An haifi biyar daga cikin 'yan wasansu ne a kasashen waje - hudu a kasar Chile inda galibin al-ummar Falasdinawa Kiristoci ne; da kuma Jaka Ihbeisheh, wanda mamarsa 'yar Sloveniya ce, amma ba ya azumi.

Ga wadannan 'yan wasan karyawa da abincin rana na ci gaba kamar yadda suka saba a otel din Plaza da ke Ramallah kuma babu wanda ya ke zama a daki daya da dan wasa mai azumi.

Yayin da yawancin 'yan wasan ke yini suna fama da yunwa, yan wasa biyar da ba sa azumi suna yini ne da fama da rasa abin yi - za su yi ta bata lokaci a dakin motsa jiki.

Wasunsu sun sauya yadda suke gudanar da harkokinsu yayi dai-dai da na takwarorinsu masu azumi, inda suke kin barci har zuwa can cikin dare da kuma barci da rana.

Lokacin cin Suhoor sai ya zama wata dama ga 'yan wasan su yi hulda da kuma barkwanci da sauran 'yan wasan masu azumi bayan atisaye da wanka da kankara da kuma motsa jiki.

Kuma dukkanin 'yan wasan sun saba da sabon yanayin gudanar da harkokinsu zuwa ranar Talatan da aka yi wasan.

Wasan da aka buga ranar karkashin wutan lantarki mai haske a filin wasan Faisal Al-Husseini ya samu halartar magoya baya 11,000 - kimanin kashi biyu cikin uku na iya yawan mutanen da filin zai iya dauka.

Jonathan Cantillana ne ya fara sha wa Falasdinu kwallo da kai, kafin Yashir Pinto Islame ya kara ta biyu.

Oman ta farke kwallo daya kafin hutun rabin lokaci ta hannun Ahmed Mubarak, amma sun kasa cimma Faladinawan.

An ayyana dan wasan Falasdinu, Yashir Pinto Islame a matsayin zakaran wasan - kuma ya yaba wa dabarar da kociyoyin tawagar tasu suka hada domin taimaka wa 'yan wasan su taka leda alhali suna azumi.

"Mun sauya atisayen saboda 'yan wasan dake azumi - kuma jami'an horar da tawagar sun yi abin yabawa. A wasan mun yi gudu sosai.

"Sabon abu ne gare ni, amma a gaskiya bai bambanta ba."