An dakatar da Oscar wasa takwas saboda haddasa fada

'Yan wasan Shanghai SIPG (a jar riga) da na Guangzhou R&F na rikici Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alkalin wasa ya kori 'yan wasa dai-dai daga kowace kungiya

An dakatar da tsohon dan wasan Chelsea na tsakiya Oscar daga buga wasa takwas saboda ya haddasa hatsaniya tsakanin 'yan wasa a lokacin da yake taka wa kungiyarsa ta China, Shanghai SIPG wasa.

Ana ganin da gangan Oscar, mai shekara 25, ya ruba 'yan wasa biyu na kungiyar da suke karawa da ita ta Guangzhou R&F a lokacin wasan nasu ranar Lahadi wanda suka yi kunnen-doki 1-1.

A dalilin haka ne sai wani ya bangaje dan wasan na Brazil ya fadi kasa, daga nan kuma sai hatsaniya ta barke tsakanin 'yan wasan kungiyoyin biyu.

An kuma ci tarar Oscarn, wanda ya koma kungiyar ta Shanghai SIPG daga Chelsea a kan fan miliyan 60 a watan Janairu, fan 4,620.

Bayan rikicin alkalin wasa ya kori dan wasan kungiyar su Oscar Fu Huan da na daya kungiyar ta Guangzhou Li Zixiang, amma kuma ba a ba wa dan wasan na Brazil ko da katin gargadi ba.

An kuma dakatar da Fu wasa shida yayin da ski kuma Li aka haramta masa wasa shida saboda rawar da suka taka a fadan.

Shi kuwa Chen Zhizhao, na kungiyar Guangzhou, wanda ya ture Oscar kasa hukumar kwallon kafa ta China ta hana shi wasa bakwai.

Kociyan Shanghai Andre Villas-Boas ya kare Oscar a kan lamarin, kuma shi ma dan wasan ya ce ba wai da gangan ya buga wa 'yan wasan kwallon ba.

Kungiyar ta Shanghai ita ce ta biyu a teburin gasar Super League ta China bayan wasa 13 daga cikin 30 da suke yi.