Juventus za ta saki Dani Alves

Dani Alves a Juventus Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dani Alves ya koma Juventus daga Barcelona a 2016

Juventus ta tabbatar za ta saki Dani Alves kamar yadda ya bukata, yayin da ya rage masa shekara daya a kwantiraginsa da kungiyar.

Shugaban kungiyar Beppe Marotta wanda ya sheda wa kafofin watsa labaran Italiya haka a ranar Laraba ya ce, dan wasan ne ya bukaci hakan domin ya je ya gwada wani wurin.

Marotta ya ce yana fata Juventus za ta cimma yarjejeniya da Alves domin amfanin dukkaninsu.

Ana ganin dai kociyan Manchester City Pep Guardiola yana da sha'awar dan wasan na Brazil mai shekara 34, wanda ya sani lokacin suna tare a Barcelona.

A shekara daya da Alves ya yi a Juventus ya dauki kofin gasar kasar ta Serie A, da kuma kaiwa wasan karshe na kofin Zakarun Turai.

Kafin wannan ya yi shekara takwas a Barcelona, inda shekarunsa hudu na farko ya yi su karkashin Guardiola, kuma a lokacin suka dauki kofin Zakarun Turai biyu da kofin La Liga uku.

Manchester City ba ta da wani dan baya kwararre bayan da ta saki Pablo Zabaleta da Bacary Sagna, wadanda kwantiraginsu ya kare.

Ana maganar cewa Guardiola yana son sayen Kyle Walker na Tottenham da shi kuma Alves, wanda ya sayo wa Barcelona daga Sevilla a kan fan miliyan 23 a 2008.