Juventus: Mun samu tayi mai armashi kan Alex Sandro

Alex Sandro a wasan Juventus da Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alex Sandro a wasan karshe na Zakarun Turai wanda Real Madrid ta ci Juventus 4-1 a Cardiff, a watan da ya wuce

Juventus ta ce ta samu ta yi mai yawa da kuma armashi a kan Alex Sandro kuma ta ce ba za ta hana dan wasan tafiya ba idan yana so.

Ana rade-radin cewa Zakarun Premier, Chelsea na son daukar dan wasan na tawagar Brazil mai shekara 26.

Kociyan Chelsea Antonio Conte shi ne ke jagorantar Juve lokacin da ta sayo Sandro a kan fan miliya 23 daga Porto a 2015.

Shugaban Juventus Giuseppe Marotta ya ce: "idan dan wasa ya yanke shawarar tafiya... Ko ya za a yi a karshe dole sai ya tafi."

Sandro ya dauki kofunan Serie A da na kalubale na Italiya da Juventus ta ci a jere a jere kuma ya yi mata wasa a karawar karshe ta cin kofin Zakarun Turai da Real Madrid, ta yi nasara.