Ingila: FA ta yanke alaka da kamfanonin caca

Tsohon dan wasan Stoke, Matthew Etherington
Image caption Tsohon dan wasan Stoke Matthew Etherington ya yi asarar fan miliyan 1.5 a lokacin da yake caca a wasanni

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta kawo karshen duk wata alaka ta daukar nauyi da kamfanonin caca ke yi da ita ciki har da dadaddiyar yarjejeniyarta da kamfanin Ladbrokes.

An dauki wannan matakin ne bayan wata uku da aka yi na nazari da sake tsarin dangantakar hukumar ta FA da kamfanonin caca.

Amma kuma hukumar kwallon ta ce za ta ci gaba da musayar muhimman bayanai da kamfanonin domin gano masu harkar wasannin da ke da hannu a cacar wasanni.

Shugaban hukumar kwallon kafar ta Ingila Martin Glenn ya yaba wa kamfanin Ladbrokes kan yadda ya karbi wannan sauyin tsari.

Shugaban kamfanin cacar na Ladbrokes Jim Mullen, ya ce sun fahimci matakin na FA kan alakar hukumar da kamfanonin caca, kuma ya ce kamfaninsu zai ci gaba da aiki da hukumar domin tabbatar da dorewar gaskiya da amana a wasanni.

An sa ido tare da bincike kan alakar harkokin kwallon kafa da caca ne a kwanan nan, bayan da dan wasan tsakiyar nan Joey Barton ya soki yadda hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dogara ga kamfanonin caca.

An dakatar da Barton, wanda ya ce shi kam caca ta zama jiki a wurinsa shiga kwallon kafa tsawon wata 18 bayan da ya amsa laifin da FA ta tuhume shi da shi na caca a kwallon kafa.