Kofin Zakarun Nahiyoyi : Chile da Jamus sun yi 1-1

Alexis Sanchez lokacin da ya ci Jamus Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sanchez ya ci Jamus kwallon da ta sa ya zama wanda ya fi ci wa Chile kwallo a tarihi - guda 38

Jamus da chile su ka tashi kunnen doki 1-1 a wasan cin kofin zakarun nahiyoyi da ake yi a Rasha a ranar Alhamis din nan.

Dan wasan Arsenal Alexis Sanchez shi ne ya ci wa Chile kwallonta minti shida da fara wasa bayan da Arturo Vidal na Bayern Munich, ya zura masa kwallon da dan bayan Jamus amma abokin wasansa a Arsenal Shkodran Mustafi ya yi katobara.

Kwallon ta sa Sanchez ya zama dan wasan da ya fi ciwa Chile yawan kwallo a tarihi, inda ya doke Marcelo Salas mai kwallo 37, da kwallo daya, kuma ya kafa tarihi domin ita ce ta 400 a gasar zakarun nahiyoyin.

Wasa ya yi nisa saura minti hudu a tafi hutun rabin lokaci sai Lars Stindl na kungiyar Borussia Mönchengladbach ya rama wa Jamus.

Sakamakon ya sa Chile ta zama ta daya a rukunin na biyu da maki 4 da kwallo uku, sai Jamus ta biyu ita ma da maki 4 amma da yawan kwallo biyu.

Australia tana matsayi na uku da maki daya da bashin kwallo daya a ragarta, yayin da Kamaru take ta hudu (karshe) da maki daya, da kuma bashin kwallo biyu.

A ranar Lahadi kasashen za su yi wasansu na rukuni na karshe, inda Kamaru za ta hadu da Jamus sai Chile ta fafata da Australia.

Kafin sannan a ranar Asabar za a yi wasan karshe na rukuni na daya (Group A), lokacin da Rasha mai masaukin baki za ta kara da Mexico, New Zealand kuwa ta hadu da Portugal.