An naɗa Mauricio Pellegrino sabon kocin Southampton

Mauricio Pellegrino Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A shekarar 2012 ne Pellegrino ya zama cocin Valencia

Kungiyar Kwallon Kafa ta Southampton ta nada Mauricio Pellegrino a matsayin sabon kocinta.

Kocin dan kasar Argentina, mai shekara 45, zai maye gurbin Claude Puel wanda aka sallame shi a farkon watan Yuni bayan ya yi kakar wasa daya.

Pellegrino ya ajiye aikin jagorancin kungiyar Alaves ne a karshen watan Mayu, bayan Barcelona ta lashe su a wasan karshe na Kocin Spain kuma suka kammala gasar La Liga a matsayi na tara.

"Falsafata da kuma tsare-tsarena za su dace sosai da kulob din Southampton," in ji Pellegrino wanda ya sanya hannu a yarjejeniyar shekara uku da kulob din.

Ya ci gaba da cewa:"So nake na rika cin wasanni, na samu nasara ta yadda zan gina kulob wanda kowa zai rika ba da gudunmuwa 100 bisa 100."

Pellegrino ya taba zama mataimakin kocin kulob din Liverpool tsakanin shekarar 2008 zuwa 2010, yayin da a shekarar 2012 ya zama kocin Valencia.

Labarai masu alaka