Alvaro Arbeloa ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa

Alvaro Arbeloa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arbeloa ya yi wa Liverpool wasa fiye da sau 200

Tsohon dan wasan Liverpool, Real Madrid da kuma West Ham Alvaro Arbeloa ya yi ritaya daga kwallon kafa.

Dan wasan mai shekara 34, wanda tsohon wasan tawagar Spain ne ya koma Madrid daga Liverpool a shekarar 2009.

Arbeloa ya taba lashe La Liga sau daya da kuma Kofin Zakarun Turai sau biyu a Madrid, kafin ya koma kungiyar West Ham a watan Agustan bara.

"Lokaci ya yi da zan yi bankwana. Har yanzu ina da karfin kara ci gaba da wasa," in ji shi.

Ya yi wa Liverpool wasa fiye da sau 200, har ila yau, ya kasance a Madrid da kuma West Ham tsakanin shekarar 2007 zuwa 2017 kuma sau 56 yana wa tawagar Spain wasa.

Labarai masu alaka