Federer ya lashe kofin Halle Open

Roger Federer wins Halle Open Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Federer ya fara lashe gasar Halle Open ne a shekarar 2003

Dan wansan tenis Roger Federer ya doke Alexander Zverev abin da ya bashi damar lashe kofin tenis na Gerry Weber Open karo na tara da ake yi a kasar Jamus.

Dan kasar Switzerland, Federer mai shekara 35, ya doke Zverev ne da ci 6-1 6-3 a mintuna 53 da fara wasan.

A bara dai Zverev, wanda dan kasar Jamus ne, ya doke Federer a wasan kusa da na karshe.

"Ban san ko zan kara samun nasara a wannan gasar ba, saboda haka farin cikin da nake ciki a yau ba ya musaltuwa," in ji Federer.

Wannan nasarar da ya samu ita ce ta hudu a bana.

Federer ya lashe gasar Australian Open da BNP Paribas Open a Indiya da kuma gasar Miami Open a Amurka duka a shekarar nan.

Labarai masu alaka