Ko Harry Kane zai iya komawa Man Utd?

Kane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kane ne dan wasan da yafi zura kwallo a raga a kakar firimiyar bara.

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya fada wa kulob din bukatar sayen dan wasan gaban Tottenham Harry Kane, kamar yadda jaridar Sunday Mirror ta bayyana.

Jaridar wadda ake bugawa a Birtaniya ta ruwaito cewa Mourinho ya ce ya fi so a saya masa Kane maimakon tsohon dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo.

Ana danganta Ronaldo da komawa Man U ne tun bayan da ya bayyana aniyyarsa ta barin kasar Spain.

Bayan da ta bayyana cewa Ronaldo zai ci gaba da wasa a Madrid ne, Mourinho ya bukaci kulob din Man U ya fara zawarcin Kane da kuma dan wasan gaban Madrid, Alvaro Morata.

Manchester United ta lashe kofin Europa wanda hakan zai ba ta damar zuwa Gasar Zakarun Turai na badi, duk da cewa ta kammala Gasar Firimiyar ba ne a matsayi na shida.

Labarai masu alaka