Chelsea na daf da sayen Bakayoko daga Monaco

Bakayoko Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bakayoko ya koma Monaco ne a shekarar 2014

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana daf da sayen dan wasan tsakiyar kulob din Monaco Tiemoue Bakayoko.

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce dan wasan mai shekara 22 zai taka muhimmiyar rawa a kulob din Chelsea.

Maganar sayen dan wasan ta yi nisa wanda zai zama dan wasa na farko da zakarun firimiyar za su saya a kakar bana.

Bakayoko yana cikin 'yan wasan da suka taka muhimmiyar rawa yayin da kulob din Monaco ya kai wasan kusa da na karshe a Gasar Zakarun Turai ta bana.

Ya koma Monaco ne daga Rennes a shekarar 2014 kuma ya fara buga wa tawagar Faransa wasa ne a wani wasan sada zumunta da Spain ta doke su a watan Maris.

Labarai masu alaka