Bertrand Traore ya koma Lyon a kan fam 8.8m

Traore Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Traore ya yi kakar bara ne a kulob din Ajax a matsayin aro

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Bertrand Traore, ya koma kulob din Lyon a kan fam miliyan takwas da dubu 800.

Traore, mai shekara 21, wanda dan asalin kasar Burkina Faso ne ya yi kakar bara ne a kulob din Ajax a matsayin aro.

Ya koma Chelsea ne a shekarar 2014 kuma ya yi wasa sau 16, inda ya zura kwallo a raga sau hudu.

A Ajax ya buga wasa sau 13 ciki har da wasan karshe na Gasar Europa da Manchester United ta doke su.

Traore ya amince da kwantaragin shekara biyar ne a Lyon.

Labarai masu alaka