Dani Alves ya bar Juventus bayan kaka daya a Italiya

Dani Alves Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dani Alves ya koma Juventus daga Barcelona a shekarar 2016

Dani Alves da Manchester City take nema ya bar zakaran Serie A, Juventus bayan ya shafe kaka daya tak a Italiya.

Alves, mai shekara 34 kuma dan asalin Brazil ya tabbatar da barin Juventus din ne ta sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Ya ce: "A yau huldarmu ta wasa ta kare kuma ba zan manta da dukkan wadanda suka sanya Juve ta kasance babbar kungiya ta hanyar soyayya da kyawawan halayaen da suka nuna min ba."

An alakanta City da sayen Alves, inda Juve ta ce za ta sallame shi daga kwantiraginsa.

Alves ya kara da cewar: "Zan so in mika godiyata ga dukkan magoya bayan Juventus, da abokan wasana wadanda suka karbe ni hannu bibbiyu yadda kwararru ke yi a madadin kungiya mai nasara."

Wasa na karshen da ya buga wa Juventus shi ne kuma wasan karshe na gasar Zakarun Turai inda Real Madrid ta doke Juventus din 4-1 a Cardiff.

Alves ya buga wasanni 33 a yayin da kungiyar ta lashe gasa biyu na cikin gida a karo na uku cikin shekara uku.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba