Ina dan Afirka na farko da ya taka leda a gasar Firimiya?

Perter Ndlovu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Peter Ndlovu ya taka wa Coventry City leda ne a lokacin babu kudi sosai a gasar Firimiya

Peter Ndlovu ya fara buga kwallon kafa ne da buga kwallon roba a kan titunan birnin Bulawayo, birni na biyu mafi girma a Zimbabwe.

A cikin irin wannan wasanni na kan titi mai kura ne Peter ya sha kwallaye 11 a wasa daya, lamarin da ya dauki hankalin kociyan matasa na kunigiyar kwallon kafa ta Highlanders da ke Bulawayo.

Lokacin ne sana'ar kwallon kafa ta Peter Ndlovu ta soma kuma ya kama hanyarsa ta zama baki dan Afirka na farko da ya fara taka leda a gasar Firimiya ta Ingila.

A wancan lokacin kungiyar Coventry City ta kai ziyara kasar Zimbabwe domin buga wani wasa gabannin kakar wasanni da tawagar kwallon kafa ta Zimbabwe da kuma kungiyar Highlanders. Dan wasan ya buga wasanni biyu, kuma jami'an Coventry City sun yi sha'awar yadda ya taka leda.

Ndlovu ya ce: "Zan iya tunawa bayan wasan, kociyan Coventry City, John Sillett, ya ce ba zan bar yaron nan a nan ba, da haka na fara sana'ar kwallo."

Ndlovu ya kara da cewa ya ji wani dadi na musamman na kasancewa dan Afirka na farko da zai fara buga wasa a gasar da za a iya cewa ta fi kowacce a duniya.

"A wancan lokacin akwai 'yan kwallon Afirka da yawa amman kasancewa dan Afirka na farko mai taka leda a gasar Firimiya ya sa na fita daban. Wannan babban abu ne. Na ji matukar dadi, na rasa abin fada domin babban abu ne," inji Ndlovu wanda ya bude hanya ga jerin 'yan wasan Afirka wadanda suka biyo bayansa kamar su Didier Drogba da Samuel Eto da Michael Essien da ire-irensu.

Dan asalin Zimbabwen ya buga wasansa na farko ne a wasan da Coventry City ta fafata da Arsenal a kakar 1991/1992 kuma ya ci kwallon da ta bai wa kungiyarsa nasara.

"Cin kwallo a wasa na farko babban abu ne ga dan wasa. Wasa zai iya yi maka kyau, amman zai fi tasiri in ka ci kwallo. Na tuna wasana na farko a Arsenal. Na shiga wasan ne a lokacin da aka yi canji kuma na ci kwallon da ta ba da nasara a wasan saboda haka abun farin ciki ne. " In ji shi.

Ndlovu ya ci kwallo 43 a wasanni 176 da ya buga wa Coventry City a tsakanin 1991 da 1997.

Ya ce duk da cewa kwallonsa ta farko tana da muhimmanci sosai, ya fifita kwallaye uku da ya ci a Anfield a ranar 14 ga watan Maris na shekarar 1995, a matsayin wasansa mafi kyau. Wadannan kwallaye sun sa ya zama dan kwallon kungiya mai ziyara ta farko da ta fara cin Liverpool kwallaye uku a Anfield tun shekarar 1962. Coventry ta yi nasara a wasan da 3-2.

"Ina tuna abubuwa da dama game da cin Liverpool, kungiyar da na goyi baya a lokacin da ina yaro," In ji Ndlovu wanda aka fi sani da sunan "Harsashin Bulawo" a harkar kwallon kafa.

Ndlovu ya shiga fagen tamaular Ingila a lokacin da ake samun matsalar wariyar launin fata tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa, amman ya ce shi bai fuskanci wani kalubale ba ta wannan fuskar.

"Babu kalubale masu yawa ta nan. Abun da ya dame ni shi ne mayar da hankali kan taka leda. Ban hadu da mutanen da suka nuna mini wariyar launin fata ba, amma akwai lokutan da masu goyon baya za su zage ka, amman ka san abun da ya kamata ka yi shi ne ka mayar da hankali a kan aikinka ka ci kwallaye sannan za su yi shiru," In ji Ndlovu.

A yanzu haka yana aiki ne a matsayin kociyan kungiyar kwallon kafa ta Mamelodi Sundowns, Zakarun Afirka masu tashe da ke birnin Pretoria, a kasar Afirka ta Kudu.

Ya ce yana amfani da dabarun da ya koya a lokacin da ya buga wa Coventry City kwallo a aikinsa na yanzu.

Ya ce dan wasan Arsenal, Lee Dickson, shi ne abokin hamayya mafi karfin hali da ya taba buga wasa da shi.

Da-na-sanin da yake yi kawai shi ne rashin buga wasa a lokacin da gasar Firimiya ke da kudi kamar yanzu.

Cikin murmushi Ndlovu ya ce "A lokacin da nake wasa akwai matukar wuya kan yadda kake shan taku, amman da zai fi kyau da a yanzu nake taka leda saboda akwai kudi mai yawa."