Ya kamata maza su rika karawa da mata a tennis - John McEnroe

John McEnroe
Bayanan hoto,

John McEnroe ya ce da Serena Williams ta biyu a duniya, a cikin maza take tennis da ta 700 za ta zama

Tsohon gwanin wasan tennis John McEnroeya bayar da shawarar a rika hada gasar da maza za su rika karawa da mata domin tabbatar da gaskiyar ikirarinsa cewa idan da Serena Williams a gasar maza take da za ta kasance ta 700 a cikin gwanayen a duniya.

McEnroe wanda ya dauki manyan kofunan tennis bakwai na duniya ya ce Williams ita ce babbar gwana a tsakanin mata amma idan da a cikin maza take to da labarin ya sha bamban.

Serena Williams mai shekara 35, wadda ta dauki manyan kofunan duniya na tennis guda 23 ta mayar wa Mcroe mai shekara 58 martani ta twitter, inda ta bukace shi da ya mutunta ta ya fita daga sha'aninta.

Bayanan hoto,

Serena Williams ta bukaci McEnroe ya fita daga sha'aninta

Shi ma dan wasan da yake matsayi na 701 a tsakanin gwanayen tennis din a duniya, dan Rasha, Dmitry Tursunov, a ranar Talata shi ma ya ce yana ganin zai iya doke Ba'amurkiya Williams, wadda ake sa ran za ta haihu a lokacin kaka.

Tursunov mai shekara 34, wanda ya taba kaiwa har na 20 a duniya, ya ce ba ya jin McEnroe yana son ya raina tennis din mata ne, amma ya ce gaskiyar lamari ita ce gaba daya maza sun fi mata karfi.