Gasar Kofin Duniya : Ingila ta bayar da cin hanci

Takardar ba wa Qatar damar gudanar da gasar kofin duniya ta 2022 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Qatar aka ba wa damar gudanar da gasar kofin duniya ta 2022 a 2010, yayin da Rasha ta samu ta gasar 2018

Shirin da Ingila ta yi na wasan sada zumunta a kasar Thailand domin kasar ta Asiya ta mara mata baya a neman karbar bakuncin gasar kofin duniya ta 2018 wani salo ne na cin hanci, kamar yadda aka sheda wa masu bincike.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila Geoff Thompson shi ne ya bayyna hakan lokacin da ake yi masa tambayoyi yayin bincike a kan batun neman karbar bakuncin gasar kofin duniya ta 2018 da ta 2022.

A ranar Talata ne hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta fitar da cikakken rahoton binciken na shekara ta 2014.

Wannan ya biyo bayan wasu bayanai na rahoton ne da aka tsegunta wa jaridar Bild ta Jamus, wadanda ita kuma ta wallafa.

Tsohon mai bincike mai zaman kansa, kan ka'idojin Fifa, Michael Garcia shi ne ya rubuta rahoton mai shafi 422.

Ya ajiye aikin domin nuna kin amincewarsa da bayyana shafi 42 kawai na rahoton nasa da aka takaita.

Wanda takaitaccen rahoton ya wanke Rasha da Qatar, wadanda suka samu ikon gudanar da gasar ta kofin duniya ta 2018 da ta 2022 daga zargin rashawa.

Amma kuma ya tuhumi abubuwan da wasu manyan jami'an Fifa da kuma 'yan kwamitocin neman karbar gasar na kasashe suka yi ciki har da 'yan Ingila.

Rahoton ya bayar da misalin wata tattaunawa da babban jagoran kwamitin nema wa Ingila damar karbar bakuncin gasar ta 2018 Thompson a kan shirin tawagar wasan Ingila na zuwa Thailand domin samun kuri'ar kasar a zaben.

Ingila ta gabatar wa Thailnad wannan dama ce ta zuwa su yi wasan sada zumuntar kwana takwas kafin kada kuri'ar a shekara ta 2010 domin zabar kasar da za a ba wa damar gudanar da gasar 2018 da kuma ta 2022.

Bayan mako uku da gabatar da tayin sai Ingila ta janye daga shirin zuwa Thailand din, wanda a lokacin an riga an kada kuri'a, wadda ta tabbatar kasar ba ta mara wa Ingila baya ba domin samun damar.