Tennis : An ba wa Geneva damar gudanar da wasan kofin duniya na farko

'Yan wasan Argentina da suka dauki kofin Davis a 2016 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Argentina ta doke Croatia a wasan karshe na Davis Cup a 2016

Hukumar kwallon tennis ta duniya ta zabi Geneva a matsayin inda za a gudanar gasar farko ta cin kofin duniya na wasan a 2018.

Gasar za ta hada da wasannin karshe na cin kofin gasar maza ta hukumar kwallon tennis ta duniya wato Davis Cup da kuma gasar cin kofin wasan mata na hukumar wato Fed Cup.

Za a yi wasan ne a filin wasa na Palexpo convention centre tsawon shekara uku daga watan Nuwamba na 2018.

Shugaban hukumar tennis din ta duniya (ITF) David Haggerty, ya ce akwai bukatar samar da canji domin cin cikakkiyar moriyar wasannin biyu masu matukar tarihi.

Hukumar gudanarwar ITF ita ce ta zabi birnin Geneva a lokacin taronta a birnin Frankfurt na Jamus, daga cikin jerin birane shida, wadanda suka hada da Copenhagen (denmark) da Miami (amurka) da Istanbul (turkiyya) da Turin (italiya) da kuma Wuhan (china).

Za a bukaci babban taron hukumar na shekara-shekara da ya amince da sauye-sauyen da aka bullo da su a yayin taron da za a yi na bana a birnin Ho Chi Minh na Vietnam, a watan Agusta na 2017.

Argentina ce ke rike da kofin Davis (na gasar maza) yayin da Jamhuriyar Czech kuma ta ci kofin Fed Cup ( na gasar ta mata) a 2016.