Zakarun Nahiyoyi: Chile ta yi waje da Portugal da 3-0

Mai tsaron ragar Chile Claudio Bravo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Claudio Bravo ne ya zama gwarzon wasan, inda ya doke dukkanin fanareti uku da 'yan Portugal suka buga

Chile ta yi waje da Portugal a wasan kusa da karshe na cin kofin zakarun nahiyoyi da ci 3-0 a bugun fanareti a gasar da ake yi a Rasha.

Bayan minti 90 da kuma karin minti 30 na fitar da gwani, ba kasar da ta zura kwallo, hakan ya sa aka je bugun fanareti.

Chile ce ta fara daukar fanaretin inda Arturo Vidal ya jefa ta a raga, sai kuma Ricardo Quaresma ya daukar wa Portugal inda golan Chile kuma dan Manchester City Claudio Bravo ya kade ta.

Aranquiz da Alexis Sancez dukkaninsu sun ci wa Chile bugunsu, yayin da Joao Moutinho da Nani suka barar da tasu, inda Claudio Bravo ya rika kade kwallon.

Wannan ne ya sa ba sai an kai ga ci gaba da bugun ba, abin da ya sa Ronaldo bai kai ga bugawa ba domin Chile ta ci uku Portugal ba ta zura ko daya ba.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Cristiano Ronaldo bai samu damar buga tasa fanaretin ba, saboda kafin a zo kansa an gama da Portugal

A ranar Lahadi Chile za ta yi wasan karshe tsakaninta da Jamus ko Mexico, wadanda su kuma sai a gobe Alhamis za a san gwani a cikinsu.

Kafin wasan na karshe za a yi wasan neman matsayi na uku tsakanin Portugal da wadda za a fitar tsakanin Jamus da Mexico.