Sunderland ta dauki sabon kociya Simon Grayson

Simon Grayson Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Simon Grayson shi ne koci na biyu da ya fi dadewa a gasar Championship ta kasa da Premier

Sunderland ta nada kociyan kungiyar Preston North End, Simon Grayson domin zama kociyanta, kuma an tabbatar da dakatar da shirin sayar da kungiyar.

A sanarwar da hukumomin kungiyar suka fitar sun ce mutumin da ya mallake ta Ellis Short zai ci gaba da daukar nauyinta da kansa, bayan da tattaunawar da ake yi da wani katafaren kamfanin Jamus kan sayen kungiyar ta zo karshe.

Daman Sunderland na neman kociyan da zai maye gurbin David Moyes, dan yankin Scotland wanda ya ajiye aiki a watan Mayu bayan da kungiyar ta fadi daga gasar Premier.

A farkon watan nan na Yuni kungiyar ta ce ta dakatar da maganar neman sabon kociya, yayin da take ci gaba da tattaunawa kan yadda za a sayar da ita.