Jermain Defoe ya sake komawa Bournemouth

Jermain Defoe Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jermain Defoe ne na bakwai a jerin 'yan wasan da suka fi cin kwallo a tarihin Premier

Tsohon dan wasan gaba na Sunderland Jermain Defoe ya koma tsohuwar kungiyarsa Bournemouth bayan da kwantiraginsa ya kare da Sunderland din.

Dan wasan na tawagar Ingila, mai shekara 34, wanda ya kulla yarjejeniyar zaman shekara uku da Bournemouth a yanzu ya ce ya ji dadin dawowa, kuma abin da zai tabbatar da zai yi shi ne cin kwallo.

Lokacin da Defoe yake matashi ya yi kakar wasa ta shekara 2000-01 a matsayin aro a Bournemouth daga West Ham, inda ya ci kwallo a wasa goma a jere.

Tsohon dan wasan naTottenham da Portsmouth da West Ham da kuma Charlton shi ne na bakwai a jerin wadanda suka fi cin kwallo a tarihin gasar Premier, inda ya ci 158 a wasa 468 da ya yi.

Defoe ya koma Sunderland a watan Janairu na 2015 bayan dan lokacin da ya yi a kungiyar Toronto FC ta Amurka.

Kuma bayan ya ceto kungiyar daga faduwa daga Premier a kakar 2015-16 da kwallo 15 ya tsawaita zamansa har zuwa 2019.

Sai dai a yarjejeniyar zamansa a kungiyar akwai sharadin zai tafi idan yana so idan Sunderland din ta fadi daga gasar Premier, wanda wannan shi ne ya ba shi damar barinta bayan da ta gama kakar da ta kare a matsayin ta karshe a tebur.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jermain Defoe ya ci kwallo 18 lokacin da yake zaman aro a Bournemouth a kakar 2000-01

Defoe ya fara taka wa Ingila leda a shekara ta 2004, kuma ya buga mata gasar cin kofin duniya ta 2010, amma kuma bai yi mata wasa ba a tsakanin 2013 da 2017.

Bajintar da yake nunawa a bana ta sa kociyan Ingila Gareth Southgate ya sake gayyato shi tawagar kasar, kuma ya ci mata kwallonsa ta 20 a wasan da suka yi da Lithuania a watan Maris, na neman damar zuwa gasar cin kofin duniya.