Lyon ta ki sallama wa Arsenal Lacazette

Alexandre Lacazette na Lyon da Faransa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alexandre Lacazette ya ci wa Lyon kwallo 100 a wasa 203, kuma ya ci wa Faransa 1 a wasa 11

Kungiyar Lyon ta ki sallama wa Arsenal dan wasanta na Faransa Alexandre Lacazette mai shekara 26, amma dai suna ci gaba da tattaunawa.

Haka kuma babu tabbas cewa Gunners din za ta samu dan wasan tsakiya na Monaco Thomas Lemar, mai shekara 21, domin a nan ma an yi watsi da tayinta.

Sannan har yanzu ba kungiyar da ta nuna wa Arsenal din bukatarta ta sayen dan wasan gaba na Chile Alexis Sanchez mai shekara 28.

Sauran shekara daya ta rage wa Sanchez a kwantiraginsa, amma kuma Arsenal din za ta iya barinsa ya tafi idan ta samu kudin da ta ga ya dace a kansa.

Sai dai kuma sakin dan wasan ya dogara ne ga wasu abubuwan, kamar irin 'yan wasan da Arsenal din ta samu da za su kara mata karfi, da kuma kungiyar da ta neme shi, domin ba za ta so ta sayar da shi ga wata kungiya ta Ingila ba.

Amma kuma duk da haka Arsenal din na fatan Sanchez, wanda shi ne ya fi ci mata kwallo a kakar da ta kare zai sabunta kwantiraginsa.