Zakarun Nahiyoyi: Jamus ta fitar da Mexico da ci 4-1

Leon Goretzka yana zura kwallo a ragar Mexico Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana rade-radin cewa Leon Goretzka zai koma Arsenal a bazara

Jamus ta kai wasan karshe na gasar kofin zakarun nahiyoyi bayan da ta doke Mexico a wasan kusa da karshe da ci 4-1, a gasar da ake yi a Rasha, a ranar Alhamis.

Leon Goretzka na kungiyar Schalke, wanda ake cewa zai koma Arsenal a bazara, wanda ya ci kwallo biyu a wasan shi ne ya fara daga raga a minti na shida da kuma na takwas da fara taka leda.

Sai kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a minti na 59, Timo Werner ya ci wa Jamus kwallo ta uku wadda ya kamata a ce ta karya lagon 'yan Mexicon amma suka ci gaba da matsa Jamusawan.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Timo Werner ne ya ci wa Jamus kwallo ta uku wadda ta sa ya zama daya da Leon Goretzka wajen fin cin kwallo a gasar-uku-uku

Sai a minti na 89 ne hakar 'yan Mexicon ta fara cimma ruwa bayan da Marco Fabian ya lalo wata kwallo daga kusan tsakiyar fili wadda ba ta zame a ko ina ba sai a ragar Jamus.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

To amma kuma zakarun na duniya ba su sarara ba domin bayan minti 90 na wasan ana shirin tashi sai dan wasan Jamus din na kungiyar Ajax, Amin Younes, ya ci musu kwallo ta karshe kuma ta hudu.

A ranar Lahadi Jamus za ta kara da Chile a wasan karshe, amma kafin sannan a ranar Portugal za ta fafata da Mexico domin samun matsayi na uku.