Watford ta sayi Kiko Femenia daga Alaves tare da Daniel Bachmann daga Stoke

Kiko Femenia Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kiko Femenia ya buga wasa sau 31 a gasar La Liga a kakar bara

Kungiyar kwallon kafa ta Watford ta sayi dan wasan baya na dama Kiko Femenia daga Alaves kan yarjejeniyar shekara hudu.

Femenia, mai shekara 26, ya fara taka leda a matsayin dan wasan gaba na gefe kuma ya yi wasa a Barcelona ajin B da Real Madrid ajin B.

Mai tsaron gidan tawagar Austria na 'yan kasa da shekara 21, Daniel Bachmann ya koma Hornests din ne daga Stoke City.

Dan shekara 22, wanda ya yi shekara shida a Potters, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar shekara uku a Vicarage Road.

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba