Willy Caballero: Chelsea ta sayi tsohon mai tsaron gidan Manchester City

Willy Caballero Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Willy Caballero ya koma Manchester City ne a shekarar 2014

Zakarun gasar Firimiya Chelasea ta sayi tsohon mai tsaron gidan Manchester City, Willy Caballero.

An sallami dan asalin kasar Ajentinan ne a lokacin da kontiginsa ya kare a karshen watan Yuni.

Caballero, mai shekara 35, ya je Ingila ne daga Malaga a shekarar 2014 kuma ya buga wasanni 26wa kungiyar Pep Guardiola a kakar bara.

Ya ce: "Na yi murnar komawa zakarun Ingila. Ina fatan haduwa da 'yan wasan in kuma taimaka wa kungiyar domin ta sake samun nasarori."

Chelsea ta sayar da mai tsaron gidan ta na biyu Asmir Begovic wa Bournemouth a watan Mayu.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba