Zakarun Nahiyoyi: Portugal ta zama ta uku bayan doke Mexico 2-1

Adrien Silva Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fanaretin da Adrien Silva ya ci wa Portugal ta yi nasarar zama ta uku a gasar

Portugal ta sami matsayi na uku bayan da ta doke Mexico da ci 2-1 a gasar cin kofin Confederations da ake yi a Rasha.

Mexico ce ta fara cin kwallo a minti na 54 bayan da dan wasan Portugal Neto ya ci kansu.

Ana dab da shirin tashi ne kuma bayan minti 90 na wasan sai Pepe ya rama da kai da wata kwallo wadda Ricardo Quaresma ya dauko.

Wannan ne ya sa aka tafi karin lokaci na raba gardama na minti 30, inda a cikin minti 15 na kashin farko Portugal ta samu fanareti bayan da Miguel Layun ya taba kwallon da hannu wadda Adrien Silva ya ci mata a minti na 104.

Portugal ta yi wasan ne ba tare da Cristiano Ronaldo ba, saboda an ba shi damar ya je ya ga tagwayen da aka haifa masa a Amurka.

Kasashen biyu sun hadu a wasansu na farko na gasar a matakin rukuni inda suka tashi 2-2 bayan da Mexico ta rama kwallo ta biyun da Portugal ta ci ta ana dab da tashi daga wasan.

Chile ce ta fitar da Portugal a wasan kusa da karshe na gasar a bugun fanareti da ci 3-0, yayin da ita kuma Mexico Jamus ta fitar da ita da ci 4-1.

A ranar Lahadin nan ne da karfe bakwai na dare agogon Najeriya za a yi wasan karshe tsakanin masu rike da kofin duniya, Jamus da kuma zakarun Latin Amurka Chile.