Ingila: Kociya ya buga wa kungiya saboda karancin 'yan wasa

Steve Claridge lokacin yana Portsmouth tsakanin 1998-2001 Hakkin mallakar hoto Empics
Image caption Steve Claridge ya ci kwallo 34 a wasan lig 104 da ya yi wa Portsmouth tsakanin 1998-2001

Kociyan kungiyar Salisbury da ke Ingila Steve Claridge ya karkade takalman kwallonsa bayan yayi ritaya yana da shekara 51, ya buga wa kungiyar a wasan sada zumunta ranar Asabar, saboda 'yan wasanta ba su cika ba.

Claridge, wanda ya taka leda a manyan wasanni sama da 1,000 kafin ya yi ritaya a 2012, ya shigar wa kungiyar tasa ne a wasan da Portsmouth ta doke su da ci 3-0.

Kociyan ya shiga ne saboda a lokacin 'yan wasan kungiyarsa ba su cika ba da guda daya, yayin da gusa biyu suke hutu.

Steve Claridge, wanda tsohon dan wasan gaba na Leicester City da Portsmouth da Millwall ne ya fara wasan kwararru ne a Bournemouth a 1984, sannan ya yi kociyan kungiyoyin Pompey da Millwall da kuma Weymouth.

Kungiyar ta Wiltshire ita ce ta 23 da kociyan wanda ke yi wa BBC fashin baki a kan kwallon kafa, ya yi wa wasa.

Kociyan ya sheda wa BBC cewa ya shiga wasan ne saboda ya zama wajibi, domin ba yadda za su yi, amma ba wai don wani abu ba ne na nuna kansa.